Bayani Akan BOLLINGER BANDS INDICATOR  – Ameenu A Sa’ad 

Bayani Akan BOLLINGER BANDS INDICATOR  - Ameenu A Sa'ad 

Wannan Blog Post Din Zaiyi Bayani Akan BOLLINGER BANDS INDICATOR  Da Kuma Yadda Ake Amfani Da BBI Da Kuma Mahimmancinta A Trading.  Ameenu A Sa’ad Yayi Kokari Wajen Saukaka Bayani Don Fahimta.

A Last rubutu nayi bayanin RABE-RABEN indicators kuma harnace idan nasamu damu Zan dauki indicator daddae a kowanne categories na indicators Nayi Bayani daedae Gwargwado. Indicator din daxamu tattauna akanta yau shine Bollinger band indicator ita tana category nhe na volatily indicator.

SHIN YAYA BOLLINGER BANDS INDICATOR TAKE??

Bollinger bands sanannan Tools Wanda Akeyin binciken fasaha dashi (Technical analysis) a financial market, John Bollinger shine wanda yaqirqireta a shekarar 1980s. Ana Amfani da Bollinger bands wajen Gwaji/Auna motsin kasuwa (volatility) dakuma gane yiyuwar siye ko siyarwa dangane da mostin farshin kasuwa.

Bollinger bands Yanada layuka guda uku ajikinsa sune kamar haka:-
i. Upper band:- a jikin Bollinger bands upper band Yana Aeki Amatsayin dynamic resistance, sannan Kuma Yana nuni da cewa kasuwa taje overbought. idan price action yatabo upper band hakan na nuna cewa ansamu Masu siyane sosae suka shigo cikin kasuwar, dayiwuwar idan kasuwa taje wannan Asamu reversal kasuwa ta juyo qasa saboda mutane xasu Fara siyarwa nhe tunda kasuwa taje overbought.

ii. Middle band:- middle band Kuma simple moving average (SMA) yawanci Yana zuwane a saetin kwana 20, ma’ana Yana lissafa average siye da siyarwar daya faruwa a kasuwa a kwana 20 din dasuka wuce nhe sae yayi ma prediction din Abunda zaefaru a gaba. Dayiwuwar idan price action yayi crossing saman (SMA) kasuwa tacigaba ta tafi uptrend, haka idan price action yayi crossing qasan (SMA) da kasuwa xata cigaba da zuba qasa wato down trend.

iii. Lower band:- Yana Aeki ne Amatsayin dynamic support, sannan Shima yana nufin cewa kasuwa taje oversold ma’ana idan price action yatabo lower band Yana nuni cewa ansamu high selling pressure ma’ana masu siyarwa sun rinjayi masu siya nhe sosae, dayiyuwar idan price action yaxo wannan gurin asamu reversal kasuwa tajuya sama saboda a wannan matakinne traders zasu Fara siya.

•YA AKEYIN TRADE DA BOLLINGER BANDS.

I. Bollinger squeeze:- Bollinger squeeze shine aduk lokacin da mostin qasuwa yaragu yayi qasa ma’ana kasuwa Tana a consolidation a lokacin upper band da lower band sukan matse da juna sakamakon rashin mostin da kasuwa takeyi. Galibi Traders suna kallon wannan squeeze din a matsayin Dama ta samun breakout Kodae kasuwa ta tashi sama (uptrend) ko Kuma tayi qasa(downtrend).

 

Duba: Bayani Akan Makomar Kasuwancin Crypto 2025 – Mohd Sheka

ii. Breakout:- A lokacin da price Action yayi breaking din lower band ko Kuma upper band hakan na nunin Alama cewa ansamu tabbacin trend Mai karfi. Misali idan price action yayi breaking upper band hakan na nunin cewa ansamu tabbacin continuation da bullish trend, haka ma idan price action yayi breaking din lower band shima yana nunin cewa ansamu tabbacin continuation na bearish trend.

iii. Mean reversion:- wasu traders din suna Amfani da Bollinger bands wajen mean reversion strategy, idan price action yatabo upper band ko kuma lower band wataqila Yana iya breaking wannan upper band ko Kuma lower band din, ko Kuma yayo reversal ma’ana ya juyo zuwa middle band shine simple moving average na kwana (20) dinnan. Misali shine
• idan price action yataba upper band hakan na nufin anje overbought ma’ana ansirsiya dayawa hakan na iya haifar da mutane xasu Fara siyarwa nhe a wannan gurin wannan damace da mutum xae iya bude short position agurin.
• idan price action yataba lower band hakan na nunin cewa ansamu oversold a kasuwar mutane sunsirsiyar nhe,hakan shine xae baka tabbacin kasuwa zata iya yin reversal ta juya zuwa middle band ko kuma tawuce zuwa upper band, saboda traders suna Amfani da wannan nhe sushigo kasuwa musamman mean reversion traders suna kallon wannan Abun Amatsayin buy opportunity.

-Hoto na farko shine yadda Bollinger band line suke.
-Hoto Na biyu shine yadda Bollinger squeeze yake
-Hoto na uku shine misalin yadda Buy/Sell

5857399888193636797 5857399888193636796 5857399888193636800 5857399888193636798

Waye Ameenu A Sa’ad ???

Scroll to Top