Bayani Akan Makomar Kasuwancin Crypto 2025 – Mohd Sheka

Bayani Akan Makomar Kasuwancin Crypto 2025 - Mohd Sheka

A Wannan Blog Post Din Zaka Fahimci MAKOMAR KASUWANCIN CRYPTO A 2025 Wanda Limamin Yan Crypto Yayi, Duk Da Yayi Wannan Bayani Bisa Fahimtarsa, Tabbas Akwai Ilimi Aciki.

 

“Wannan rubutu da zanyi tunani nane da kuma hangena acikin wannan sabga tamu ta cryptosphere. Maganar gaskiya abinda nake ji yanzu shi na ji a lokacin matsanancin bearmarket na 2022-2023”

Yana da wuya ace munsake cin moriyar Bull run ko kuma tunanin cewa bull run na iya zuwa ƙarshe nan ba da daɗewa ba. Yawancin altcoins sun yi tashi na ban mamaki bayan nasarar Donald Trump, sannan akayi retrace, wannan alama ce me kyau. Kowa ya dauka hakan dai tsari ne na crypto.

A farkon 2025, A ilimance ya kamata ace Altcoins sun mike. Amma hakan bai faru ba. Me yasa? Dalilin shine: Mutane suna ta canza sheka daga memecoin zuwa wani Memecoin din. Gaba daya Fundamental yadena aiki. Zuwan pumpun gaba daya ya canza narrative na kasuwar crypto. Yazamana kasuwa ta zama kashi biyu zalla. Ta masu fundamental BTC da kuma ta masu kayan gwari (MEMECOIN)

Gaba daya LIQUIDITY ya rabu gida biyu: BTC & MEMECOIN. Altcoins ko maganarsu ba ayi. Balle abun Banza ETHEREUM, Me dakon XRP ko TRON yafi ka samun riba. Kwata kwata babu SHARED LIQUIDITY akasuwar.

Kwatsam sai kawai aka ƙaddamar da $TRUMP kuma ya shanye liquidity daga on-chain gaba daya. Wanda hakan bawai wata babbar matsala ba ce. Mafi akasarinmu mun dauka cewa ribar za ta juyo zuwa sauran altcoins. Sai kuma mai afkuwa tasake afkuwa.

 

Duba: Bayani Akan ON BALANCE VOLUME INDICATOR – Ameenu A Sa’ad

 

Matar gidan Shugaban Amurika MELANIA TRUMP,sai ta sake ƙaddamar da $MELANIA Token , abu kuma sai ya zama hauka.Itama sai ta sake janye LIQUIDITY daga kasuwar. Wannan yasa Altcoins suka sake retracing to almost 90% ko fiye.

Volume ya ragu matuƙa. Mun koma daga “alt season na gab da faruwa” zuwa “kasa kawai ake tafiya” . Kuma wannan duk yana faruwa kafin BTC ma ya fara faɗuwa. Ba abin mamaki ba ne ganin cewa kowa a Space dinnan yana cikin bakin ciki.

Yan crypto na BLAMING din INFLUENCER saboda yabasu token na holden kuma suna cikin asara. Abinda dayanmu basu gane ba shine: Zakayi fundamental da Technical analysis dinka 100% a sabgar nan. Narrative guda daya ko TREND guda daya sai duk ya bata maka lissafi.

Wannan baya nufin wai bincike ba daidai bane, a’a; kawai haka kasuwar tamu take. Dole kazama updated akan duk abinda yake faruwa. Kuma dole kayi amfani da reality din dayake gabanka.

Har yanzu ban yarda mun kai kololuwa ba, amma wannan shine mafi wahalar cycle da na taɓa fuskanta cikin shekaru 6 da suka gabata. A baya, altcoins season kusan tabbas ne. Ka zaɓi token, ka riƙe shi, kuma ka samu riba. Amma yanzu ba haka abun yake ba.

A Yanzu? Yanayin kasuwar tazama kamar caca ne ,wanda mafi yawancin lokaci asara tafi yawa. Musamman ga wadanda basu fuskanci kasuwar ba.

Wanda indai hakan taci gaba da faruwa dole liquidity yabar kasuwar, wannan kuma alamace ta BEAR SEASON.

Waye Muhammad Sheka (Imamu Sheka)

Waye Muhammad Sheka (Imamu Sheka)
Waye Muhammad Sheka (Imamu Sheka)

Muhammad Sheka Shine Founder Na BRITEC AFRICA, Kuma Malami Ne A Fannin Crypto, Masani ne Akan DEX TRADING, Influencer A Arewa.

Scroll to Top