Bayani Akan ON BALANCE VOLUME INDICATOR – Ameenu A Sa’ad

Bayani Akan ON BALANCE VOLUME INDICATOR - Ameenu A Sa'ad

A Wannan Article Din Ameenu A Sa’ad Yayi Bayani Akan ‘On Balance Volume Indicator, Tabbas Wannan Rubutun Nada Mahimmanci Ga Traders, Don Zasu Sami Zallar Ilimi.

Shin kokasan cewa volume Yana iya Riga price motsi a akasuwa??? Smart trader Suna Amfani da volume based indicators kamar OBV Wajen gane boyayyen buying Ko selling pressure dayake faruwa a kasuwa kafin price action Yanunama hakan.

 

On balance volume (OBV) volume indicator
On balance volume (OBV) volume indicator

On balance volume (OBV) volume indicator Che wacce Ake Amfani da ita wajen yin Technical analysis Akan wani cryptocurrency. Tana Auna girman siye da siyarwa nhe dayake faruwa Akan coin/token dakazo yin technical analysis Akansa. OBV cumulative indicator Che saboda kullum tana cigaba da qarawa da kuma rage volume akanta based on motsin farashi nakasuwa.

Ma’ana shine idan closing price nayau inda kasuwa tarufe kenan yafi na jiya wato inda kasuwa tarufe jiya kenan toh OBV zata qara wannan volume dinne akanta. Haka zalika idan akasin haka yafaru ma’ana closing price na yau yayi qasa dana jiya to OBV zatayi subtracting na wannan volume din akanta. Haka kuma ida motshin farashi na kasuwar bae canxaba to itama bazata chanja bah.

Duba: Menene Web3: Amfani Da Banbancin Web3 da Web2 & web1

PSYCHOLOGY DIN DAYAKE QUNSHE AGAMEDA OBV……

OBV an qirqireta abisa idea nacewa volume shine yake ainahin ra’ayi na mutane dake cikin kasuwa kafin price action Yanuna. Dalili kuwa shine:-
1. Idan banyan investors/whales suka Fara accumulation din volume Akan coin/token sunayine cikin salon da baza’agane bah saboda price action baxaeyi reacting da wuri bah wanda hakan shine xae janyo OBV yatashi Sama kafin price action yatashi tukunnah. Zakalika idan suka Fara siyarwa Suna siyarwa cikin salon da price action baxaenuna da wuri ba ayayin dakuma ita OBV zatayi dropping qasa kafin price action.

2. Yawancin Ratail traders su Suna la’akarine da price action Kae tsaya batare da Duba volume, ita kuma OBV tanuna Abunda Smart money/Big investors/ whale sukeyine kafin price action Yanunama hakan. Saboda Ko exchangers Suna irin wannan manipulation din qasa price action yanatayin Saman bayan kuma Anfara samun weak momentum na buying a wannan lokacin.

3. Divergence a matsayin gargadi Ga traders Akan su siya Ko kuma su siyar. Divergence din Kashi biyu sune kamar haka:-
a- Bullish divergence:- idan OBV tana tashi Sama shikuma price action Yana nuna Mah kasuwa tana qasa hakan na nufin Big investors/ smart Money/ whales Suna accumulation na volume nhe.
b- Bearish divergence:- shikuma shine idan OBV Kaga tafarayin qasa zuwa downtrend shikuma price action Kaga Yana tafiya Sama wanna Sell signal nhe Ansamu weak momentum na buying saboda whales da big investors sunfara siyarda da wannan assets dinne.

YADDA ZAKAYI AMFANI DA OBV WAJEN YIN TRADE SHINE:-

1. Trend confirmation:- a duk lokacin zakaga On balance volume indicator tana tafiya daedae na price action hakan Yanuna strong trend nhe either uptren Ko kuma downtrend yadanganta da inda price action din yayi dae. Idan Kaga kasuwa tana Uptrend OBV Kaga shima Yana Uptrend hakan Yanunama strong Bullish momentum haka zalikawa idan kasuwa tana downtrend shima OBV Yana tafiya downtrend shima strong bearish momentum nhe.

2. Spot Divergence:- Divergence shine kamar yadda Nayi Muku bayani idan akasamu sabani tsakanin OBV dakuma price action wannan Yana indicating na za’a reversal a akasuwa, idan kasawa tana tafiya uptrend akasamu negative divergence to zatayi reversal nhe zuwa qasa haka idan kasuwa tana tafiya qasa akasamu bullish Divergence namma za’asamu reversal nhe a kasuwar.

NOTE:- Ba’a trading da indicator guda daya zaka iya hada OBV da sauran indicators Din danayi abayanisu a Rubutun Abaya irinsu Bollinger band dakuma Williams % range Domin qarin samun confirmation mae qarfi.

Shin kataba Amfani da On balance volume indicator OBV wajen Shiga trade? Idan kataba Amfani da ita rubutamana ra’ayinka akanta a comment section….!!!

Waye Ameenu A Sa’ad 

5857399888193636794

Ameenu A. Sa’ad Daya Daga Cikin Matasan Da BRITEC ACADEMY Ta Rainane, Wanda Yake Kwarewa A Fannin Crypto Da Blockchain, Ya Sami Horo Daga Hannun Manyan Masanan Trading Na Crypto Na Arewa, Kuma Shi Kansa Ya Kasance Mai Kwazo.

Scroll to Top