Kasuwancin cryptocurrency na da matuƙar mahimmanci a zamannin mu, amma yawancin mutane—musamman a Arewacin Nijeriya—basu fahimci yadda ake yin shi ba. “Sirrin Crypto” littafi ne da na rubuta domin sauƙaƙa fahimtar cryptocurrency ga duk wanda yake son shiga wannan kasuwa.
An rubuta littafin cikin tsarin Eng-Hausa (Turanci da Hausa) domin sauƙaƙe fahimta ga masu jin Hausa, tare da ba su damar ƙara bincike. Tabbas, wannan littafi zai taimaka wa masu karatu su:
- Fahimci cryptocurrency cikin sauƙi.
- Koya dabarun ciniki don samun riba mai yawa.
- Guije wa asara ta hanyar amfani da ingantattun dabaru.
Menene Ke Cikin Littafin “Sirrin Crypto”?
Littafin ya ƙunshi sassa uku masu mahimmanci:
1. The Art of HODLing
Wannan sashe yana bada cikakken bayani game da:
- Menene cryptocurrency? Tarihinsa, ma’anarsa, da rarrabuwarsa.
- Fa’idodin cryptocurrency da yadda ake cinikayya da shi.
- Muhimman abubuwa da ya kamata mai farawa ya sani kafin shiga kasuwa.
Wannan sashe ya dace musamman ga masu farawa.
2. Cryptocurrency Analysis
Don masu ɗan gogewa, wannan sashe yana koyar da:
- Fundamental Analysis: Yadda ake tantance ingancin coin kafin saye.
- Technical Analysis: Yadda ake gano alkiblar farashin coin a kasuwa.
- Yadda ake guje wa jabun coin da kuma lokacin da ya kamata a sayi ko sayar.
Wannan zai taimaka maka rage asara kuma samun riba mai yawa.
3. Cryptocurrency Trading Strategies
A nan za ka koyi:
- Mafi kyawun lokutan saye da sayarwa.
- Yadda ake tsara jari don riba mai tarin yawa.
- Kyawawan halaye da ya kamata mai ciniki ya ɗabi’a.
- Munanan halaye da ya kamata a guje wa su.
- Wasu sirri na musamman waɗanda ƴan kasuwa da yawa ba su sani ba.
Wannan sashe zai canza kasuwancinka gaba ɗaya!
Dalilin Da Yasa Dole Ka Samu Wannan Littafi
- Sauƙaƙe fahimta: Ko da kana da ƙaramar ƙwaƙwalwa, za ka fahimci abin da aka rubuta.
- Taimako ga Arewacin Nijeriya: Littafin zai rage talauci ta hanyar ba da ilimin samun riba.
- Guida zuwa nasara: Ka koyi yadda ake ciniki da hankali don guje wa asara.
“Sirrin Crypto” shine madaidaicin jagora don duk wanda yake son shiga kasuwancin cryptocurrency ko kuma ya inganta basirarsa. Idan kana son fara ciniki da ƙafar dama, rage asara, ko samun riba mai yawa, to wannan littafi ne zai kawo maka sauyi.
Nasir I. Mahuta: Ƙwararren Masanin Fasahar Zamani, Cryptocurrency, da Kasuwancin Intanet

Nasir I. Mahuta ɗalibi ne na ilimi, masanin bincike, kuma ƙwararren mai fasaha a fannonin zamani. Shi ne mamallakin Kamfanin Sa’a Ltd, kuma yana cikin manyan ƴan kasuwar intanet (digital marketing) a Arewacin Nijeriya tare da shaidar ƙwarewa daga Google.
Bugu da ƙari, shi ɗalibin blockchain ne daga Jami’ar California, Irvine, kuma yana da Diploma a fannin cryptocurrency daga Alison. A halin yanzu, yana ɗaya daga cikin fitattun masu ba da shawara kan cryptocurrency a Arewacin Nijeriya, inda ya horar da fiye da matasa 3,000 kan yadda ake cinikin crypto da samun riba.
Fasahar Software da Kamfanin Sa’a Ltd
Nasir I. Mahuta ƙwararren software developer ne, wanda ya kafa kamfanin Sa’a Ltd don ba da sabbin mafita ta fasaha. A ƙarƙashin jagorancinsa, kamfanin yana ba da:
- Ƙirƙirar software masu sauƙi da inganci.
- Sabbin mafita ga ƙungiyoyin kasuwanci da na sirri.
- Horarwa ga matasa kan fasahar zamani.
Ƙwarewa a Digital Marketing (Kasuwancin Intanet)
Nasir ya sami shaidar ƙwarewa daga Google, wanda ke nuna cewa yana da gogewa sosai a fannin:
- Tallan kan Google (Google Ads)
- Tallan kan soshaiyal midiya (Social media marketing)
- Haɓaka kasuwanci ta hanyar intanet
Wannan ya sa ya zama jagora a fannin digital marketing a Arewacin Nijeriya.
Bincike da Ƙwarewa a Blockchain da Cryptocurrency
Nasir ya kammala gajeren karatu na blockchain daga Jami’ar California, Irvine, sannan ya sami Diploma a fannin cryptocurrency daga Alison. A matsayinsa na ƙwararren masanin crypto, yana:
- Ba da shawarwari kan yadda ake cinikin kuɗin dijital.
- Horar da matasa kan hanyoyin samun riba ta cryptocurrency.
- Bayar da sabbin dabaru don gujewa asara a kasuwar crypto.
Shi ne jagoran cryptocurrency a Arewacin Nijeriya, inda ya taimaka wa sama da 3,000 matasa su fara kasuwancin su da ƙafar dama.
Kyaututtuka da Nasarori
- Google Certified Digital Marketer
- Dalibin Blockchain (Univ. of California, Irvine)
- Diploma a Cryptocurrency (Alison)
- Horar da Matasa 3,000+ kan cryptocurrency
- Fitaccen Mai Ba da Shawara a kasuwancin crypto
Nasir I. Mahuta ƙwararren masani ne a fannonin fasaha, kasuwancin intanet, da cryptocurrency. Ta hanyar kamfaninsa Sa’a Ltd, horar da matasa, da gudanar da bincike, ya ba da gudummawa mai mahimmanci ga ci gaban fasaha da tattalin arziki a Arewacin Nijeriya.
Allah Ya Gafarta Masa.