Boc Madaki Yana Cikin Manyan Mawakan Hausa Hip Hop Na Duniya, Kafa Kyakkyawan Tarihi Ba Sabon Abu Bane Gareshi. Amma Wannan Tarihi daya Kafa Abun Alfahri Ne Ga Duk Wanda Yakeson Ganin Arewa Akan Gaba.
Ranar 22nd December, 2024. Boc Madaki Ya Saki Sabon Album Wanda Yake Cike Da Wakokin Hausa Hip Hop Masu Ma’ana Tareda Dadi, Wannan Album Din Mai Suna ‘EVERYTHING MUSIC’ Ya Cancanci Yabo Ba Iya BOC MADAKI Daya Hada Album Dinba, Har Artists Din da Suka Wakokin Tare, Acikin Wannan Artists Akwai Emperor Bling, Namenj, Jesse Jagz, Concept Man, Magnito, Krisskillz Da Sauran Mawaka Masu Hazaka. (Saurari EVERYTHING MUSIC ALBUM)
BOC MADAKI Ya Shiga Jerin Mawakan Duniya Wanda Suka Iya Tsara Kalamai A Waka (Best Lyrists Award)

Duk Wanda Yasan BOC, Yasanshi Da Iya Tsara Zance A Cikin Waka. Domin Haka Da Yawa Daga Cikin Masoyansa Suke Cewa Yafi Kowa Lyrics A Hausa Hip Hop.
Abun Alfahri, BOC MADAKI Ya Shiga Cikin Jerin Wanda Kaddamar Domin Cin Kambun Wanda Yafi Kowa Iya Tsara Kalamai A Cikin Waka na Shekarar 2024/2025. GMA Awards Sun Saka BOC MADAKI Cikin Jerin Manyan Mawakan Hip Hop Na Africa Wanda Duniya Take Ji Dasu Wajen Waka Da Iya Kalamai A Cikin Waka.
BOC MADAKI Zai Kara Da Manyan Mawaka Kamarsu ‘Reminisce‘ Wanda Ya Kasance Abokin Olamide, Oga IllBliss, Abokin M.I Abaga, Dandizzy Wanda Ake Cewa Yafi Kowa Iya FREESTYLE A Africa, JeriQ Matashin Dake Tashe A Fannin HipHop Rap Ta Nigeria, Vector Abokin Su Phyno Da Sauran Manyan Mawakan Duniya. Wannan Kadan Daga Cikin Mawakan Da BOC MADAKI Zai Kara Dasu Wajen Daukar Wannan Kambu Mai Cike Da Tirihin Gaske.
Shin BOC MADAKI Zai Iya Daukar Wannan AWARD Din Na Best Lyrist ?
Amsar ita Eh, Kuma Ya Cancanci Yaci Wannan Award, Amma Yana Bukatar Support Dinku. Tabbas A Wannan Lokacin BOC MADAKI Yana Bukatar Goyon Bayan Duk Wani Dan Arewa Kuma Mai Goyon Bayan Arewa, Kuma Mai Son Ganin Ci Gaban Arewa.