Wannan Article Zai Taimaka Maka Ka Fahimci Menene Web3, Sannan Zaka San Mahimmancin Web3, Zakasan Mene Web2, Zakasan Menene Web1.
Wannan Rubutun Kwararru A Fannin Web3, Blockchain and Cryptocurrency Ne Suka Taimaka Wajen Samar Dashi. Miracle Jeremiah Ogbuehi Da Kuma Barrister Abdul-Hadee Isah Ibraheem Sune Suka Samar Dashi.
A yanzu haka muna cikin zamanin Web3 (web three), wato Web3 Era. Menene Web3 ?
๐ ๐ฒ๐ป๐ฒ๐ป๐ฒ ๐๐ฒ๐ฏ๐ฏ?
Banda labarai dake zuwa daga twitar Elon Musk, web3 na cikin kalmomin da aka fi amfani da su a yanar gizo. An san dashi saboda alkawarin sa na gaba, gaskiya ne. Sai dai yawancin mutane basu gane shi ba. A wannan rubutun, zanyi bayani akan kalmar “WEB3”, kuma abun da yasa ta banbanta da tsarin yanar gizo na da.
๐ฌ๐ฎ๐ป๐๐, ๐บ๐ฒ๐ป๐ฒ๐ป๐ฒ ๐๐ฒ๐ฏ๐ฏ ๐ฎ ๐ธ๐ฎ๐น๐บ๐ฎ๐ฟ ๐ด๐ฎ๐๐ธ๐ฒ?
Kawai, tsarin yanar gizo na uku ne. Kamar irin wadda aka kayyata ko kuwa sabunta tsarin yanar gizon da zai tayamu muyi abubuwa dayawa kuma musamu dayawa a matsayin mutane. A matsayin mai amfani da android ko iPhone, na san kun ga tallan sabunta apps din na wayoyinku ba so daya ba. Sabunta apps din zai sa ku iya amfani da tsarin apps din , kuyi aiki dayawa kuma ku cinma burin ku da yawa.
A kowani sabuntarwa ya banbanta da masu hada apps din da kamfani, akwai bidiโar gyara ta matsalolin da masu amfani ke fuskanta. A misali, Whatsapp na shekarar 2018 bashi da kayaki ko ๐ญ๐๐๐๐๐๐๐ din whatsapp na yanzu. An sabuntashi.
To kuyi tunanin WEB3 a matsayin app na wayoyin ku da aka sabunta. Banbancin kawai shine WEB3 haryanzu na matsayin jinjirine ko kuwa ba a dade da kirkiro shi ba. Aiki ne da ake kan kayatarwa ba kamar sauran apps din ba. Akwai abubuwa dayawa da web3 za tayi da baโa gano ba. Duk dahaka, ya kamata mu sani kuma mu gane bayanai akan sa. Yanda zaโa yi, ya kamata ku san yadda aka samu web3.
๐ง๐ฎ๐ฟ๐ถ๐ต๐ถ๐ป ๐๐ฒ๐ฏ: ๐๐ฎ๐ฑ๐ฑ๐ฎ ๐ฎ๐ธ๐ฎ ๐ธ๐ฎ๐ถ ๐๐ฒ๐ฏ๐ฏ
Yanar gizo ta duniya (www) na cikin abin da aka yi amfani a yanar gizon. Da shi zaka iya zama a ko ina a duniya kuma ka iya shiga bayyananniyar yanar gizo. Tunanin yanar gizon duniya (www) ya hadu daga Tim Berner Lee a 1989. Sakamakon aikinsa ya bayyana ne a 1990. Shine muke kira ๐๐ฒ๐ฏ๐ญ.๐ฌ. tunanin shi shine wai ya tsara hanyar raba bayanai ba tare da kariya ba. Wannan na nufin, wai yanki da mutun yake, ba zai zama matsala ba wajan raba bayanai.
Hadin ๐๐ฒ๐ฏ๐ญ.๐ฌ shine ya kawo tushen web nagaba.
Tunanin na da kyau saboda raba bayanai da sanarwa zuwa ga duk duniya ba iya tsada ne dashi ba sannan ma baya cin lokaci. Ku yi tunani ku dalibai ne kuna bincike kan majalisar dinkin duniya kuma babu web, yana nufin zaku tafi har Geneva ne da samun bayanan da kuke nema. Baza ku yi tunanin hakaba, ko?
Saboda haka gyaran Berner ta samar da web na da amfani a 1990, yadda aka kaddamar da farkon tsarin web.
๐ช๐ฒ๐ฏ ๐ญ.๐ฌ
Anan, masu amfani kawai iya karba bayanan zasu yi. Ba zasu iya rabawa juna tunanin su ba. Masu amfani ba zasu iya tattaunawa ba. Kuma bazu iya hado wasu abu ba. Kawai karantawa zasu iya yi. Shi yasa ake kiran wannan web din web na karatu kawai. Ta kai daga 1990-2004. A 2004 tsarin na biyu aka kaddamar.
A Fahimtar Barrister Abdul-Hadee: Web1 ko (web one) wani lokaci ne da aka yi a shekarun baya, alakar mutane da internet shine su shiga su karanta abunda aka rubuta kadai, a wancan lokacin babu wani abunda zaka iya yi a online sai dai ka karanta abinda aka rubuta akan Google ko website ko blog.
~ Ana kiran wannan zamanin da (Read Only), Masana tare da masu bincike suna cewa zamanin Web1 ya fara ne daga 1990 har zuwa 2002.
A wadancan shekarun mutane babu social media irin na yanzu, babu kafofi irin Facebook, Twitter, Telegram, Instagram da sauran su, sa’annan babu harkar Crypto ko Blockchain.
~ Alakar mutane da internet shine su karanta, su kwafa (copy) daga Internet, ana kiran zamanin da Read Only or (You can only Read from the Internet).
๐ช๐ฒ๐ฏ ๐ฎ.๐ฌ
Wannan shine tsarin da muke amfani dashi ayanzu. Zaku iya rabar da bayanai da kan ku. Rabarda bayanai bawai sai kamfani ba. Zaku iya tattaunawa da masu amfani dashi. Zaku iya rabarda shawararku kan wani mauduโi da kamfani.
Wana tsarin yanar gizon ta kasance jagoranta ce, da samauwar shafukar sadarwa, da girmaman manyan kamfanonin fasaha kamar ๐ ๐ฒ๐๐ฎ (wanda ta ke da facebook), twitter da tallulluka wanda bayane ke samar wa.
Dunkulewa na nufin wasu mutane ne masu shi, wanda su ke san Abun da zai faru ko ba zai faru da ku ba. A sauki zaโa hana ka hawa twitter saboda ka saba dokan su. Hanya shigan ka ma zaโa iya dakatar da ita ko a kule ta. Idan hakan yafaru, za ka rasa kayi duka ayukan dake ci lokutan ka da arzikin ka a kansu. Kuma, za’a kirkiru dokoki ba tare da yardan ku ko shawaran ku. Ko menene kamfani fasahar su ke nema, sai dai in sun gadama sun canza. Matsalar shine wai kuna karkashin rashin mutumcin kamfanonin fasahan.
Da samar da dandalin da kowa zai iya raba bayanai, mutane dayawa suka fara shiga da Kuma amfani da web. Da hakan ya faru, sun bayar da bayanan su da kamfanin fasahan, suke siyar masu shi dan samun kudi. Shi ake kira “tallan na bayanai”.
Tala na bayyanai da kasuwanci kalmomi ne da ke fassara yadda kamfanonin fasaha kamar Meta suke amfani da bayanan mutane na masu amfani dan taya sauran kamfanonin su kai inda suke so su kai a kasuwa. Idan kukayi amfani da kayan Meta, cikin algorithm zai iya ciro abinda kuke so, abinda bakwa so, abun da zai ja muku hankali da wanda bai zai ja muku hankali ba. Da wannan bayanai, tallullukan da zasu dinga fito muku akan abin da kuke so ne. Matsalar shine wai ba tare da nemar izinin mu ake yi. Kuma, manyan kamfanonin fasaha suna samun riba sosai ba tare da rabbamana hakin mu.
Fahimtar Barrister Abdul-Hadee Akan Web2: Web2 wani lokaci ne da aka yi ko ake kanyi tun daga wajejen 2002 har zuwa yau, alakar mutane da Internet shine su karanta kuma su tofa albarkacin bakin su, ana kiran lokacin da (Read and Write). Wato abinda zaka iya yi da internet shine zaka iya karanta abinda aka rubuta, kaima zaka iya rubutawa a karanta.
~ Shine zamanin social media, wato social media era. A zamanin Web2 an baka dama zaka iya karantawa kuma kaima ka tofa albarkacin bakin ka.
A Web1 baka da ikon rubuta komai, sai dai ka mallaki website kaima ka rubuta naka, while a Web2 period an baka dama zaka iya rubutawa wato zaka iya comment a karkashin abunda aka rubuta.
๐ฆ๐ฎ๐ถ ๐ช๐ฒ๐ฏ ๐ฏ.๐ฌ
Ba kamar web1 da web 2 ba, web 3 are rarrabatake. Bawai na wasu mutane bane, kamfanonin fasaha ko gwamnati. An gina cikin fasahar blockchain. Wanar fasahar ce ta mai dashi a rarrabe.
Fahimtar Barrister Abdul-Hadee akan Web3: Zamanin Web3 shine zamanin da ake kira da (Read, Write and Earn).
Wato zaka karanta abinda aka rubuta akan Internet, zaka rubuta naka kaima, sannan zaka samu Kudi da Internet din.
~ Kowa da kowa a yanzu ya bar Web1, babu kowa a Web1, Web2 kuma a nan ne ake da yawa, wato majority na mutanen duniya suna cikin Web2 ‘yan kadan ne suka wuce zuwa Web3, wato Blockchain and Crypto Currency Era.
Idan ka lura da Web1 zaka ga cigaba ne na Internet din da ada ake amfani dashi babu website babu blogs babu Google ko wasu search ๐ย engines. Sai aka samu cigaba aka kawo websites da Google a 1998 da sauran su, karatu kawai zaka iya yi a Online a wancan lokaci, ba zaka iya rubutawa, ba zaka iya yin comment ko ka bayyana ra’ayin ka ba.
Web2 kuma cigaban Web1 ne, a Web2 zaka iya rubuta ra’ayin ka a Facebook, zaka yi comment idan wani ya rubuta, zaka yi haka a Facebook, Twitter, Telegram, Instagram da sauran su.
~ Amma wadannan kamfanonin su Facebook ko Meta duk suna karkashin wasu mutane ne ‘yan tsiraru, su suke kwasan makudan kudade ba tare da kowa yasan komai ba.
Sai aka fadada fasahar Web2 zuwa Blockchain and Crypto Era, wato ko baka mallaki Facebook ba zaka iya samun Kudi, ko baka mallaki Twitter ba zaka iya samun Kudi.
~ Misali, a duk social media bana samun Kudi da kowane social media sai Telegram, kudaden da suke biya a kullum, a duk 24 suna biyana ta cikin TON a Telegram revenue.
Da ace zan fadin abinda nake samu a Telegram duk 24 hours da yawa zasu ce wallahi karya ne…ย Saboda ba kowa yasan karfin Web3 da yadda abubuwan suke gudana akai ba.
Ba mining nake yi suke biyana ba balle kace kaza da kaza, da ace yau zan shafe shekara guda ban bude Telegram ba zasu cigaba da biyana sai dai duk ranar dana bude in cire Kudi na idan ina so.
Fatan mu shine a cigaba da karatu da bincike akan wadannan abubuwan.
Akwai wadanda a TikTok suke samun Kudi, wasu Facebook Reals, wasu Instagram da sauran su.
Hawa social media da kake yi makudan Kudi suke samu da kai, toh ana biyan wadanda suka cike ka’idar ne da Coins ta hanyar amfani da Blockchain, abun nan da ake ta ce muku Chacha ne ko Haram…
~ Wasu suna biya ta Dollar Accounts da sauran hanyoyi, amma Blockchain din yafi sauri ne kamar kyaftawar Ido.
๐ ๐ฒ ๐๐ฎ๐๐ฎ ๐๐ฒ๐ฏ๐ฏ ๐ฑ๐ฎ๐ฏ๐ฎ๐ป๐ฐ๐ฒ, ๐ธ๐๐บ๐ฎ ๐๐ฎ๐ณ๐ถ ๐ณ๐ถ๐๐ฒ ๐ฑ๐ฎ ๐๐๐ฎ๐ฟ๐๐ธ๐ฎ๐ป ๐ฏ๐ฎ๐๐ฎ?
1. ๐๐ป ๐ฟ๐ฎ๐ฟ๐ฟ๐ฎ๐ฏ๐ฎ:
Ba a dayanta shi ba ko ace mutum daya ne mai juya shi, ko kamfanoni ko gwamnati
2. ๐ญ๐ฎ๐ถ ๐ฏ๐ฎ๐ฟ๐ธ๐ฎ ๐ธ๐ฎ ๐ธ๐ฎ๐ฟ๐ฎ๐ป๐๐ฎ, ๐๐๐ฎ๐ฟ๐ฎ ๐ฑ๐ฎ ๐บ๐ฎ๐น๐น๐ฎ๐ธ๐ฎ
Cikin web 3, zaka iya abin da ka keyi da web1 da web2 a tsauki. Harma zaka iya yin fiye da Hakan ma. Zaka iya zaban wanda kake so ya samu bayanai da kuma wanda baka so ya same shi.
3. ๐ญ๐ฎ๐ถ ๐ฏ๐ฎ๐ธ๐ฎ ๐ถ๐ธ๐ผ๐ป ๐ฑ๐ฎ ๐ธ๐ฎ ๐ฐ๐ฎ๐ป๐ฐ๐ฎ๐ป๐๐ฎ
Idan kai kake shawara, to kai na shugaba. Abin da web3 zai iya kenan. Za a saka a cikin kuma za ka kasance cikin masu yi.
A takkaitacce, web3 shine babban abu a samurwa web mai zuwa. Yana magance matsalolin da ake fuskanta a web2 da alkawarin fiye da haka.
A rubutun gaba zai yi Magana kan fasahan Blockchain, da fasahan da aka gina web3.

Product and Developer Marketing ย BD ย Scaling Tech Solutions, Marketing, business development, and customer relationship management professional with over 4 years of experience.
Barrister Abdul-Hadee Isah Ibraheem

Masani Akan Blockchain, Masani akan Qur’ani, Malami A Fannin Web3 Da Cryptocurrency. Barrister Ya Hidimtawa Arewa Wajen Ganin Mutanen Arewa Sun Fahimci Menene Web3, Blockchain Da Crypto.