Ahmad XM Ya Bayyanawa Duniya Cewa Nafi Karfin Nai Muku Karyar Na Manta Da $70K A Wallet – Ahmad XM Yayi Martani Ga Masu ganin Karya yake.
Anata Cecekuce A Duniyar Crypto Din Arewa A Shafin Sadarwa Na X, Inda Ahmad XM Yayi Wani Tweeting Wanda Ya firgita Wasu, Ya Bawa Wasu Dariya, Wasu Na Ganin Gaskiya Ne Wasu Na Ganin Abune Mara Yuwuwa.
Farkon Wannan Satin Ne Mashahurin Dan Crypto Dinnan ‘AHMAD XM’ Ya Wallafa Wani Post A Shafinsa Na twitter Inda Yake Cewa Ya Dauko Wata Tsohuwar Samsung Dinsa Da Niyyar Zai Bawa Daya Daga Cikin Ma’aikatansa Na ACADEMY Dinsa, Kawai Saiya Duba OKX Wallet Dinsa Sai Yaga Kimanin Dalar Amurka Dubu Saba’in (71,901 USDT) A Ciki Inda Ya bayyana Cewa Ya Manta Da Ita A Ciki.
A Cikin Comments A Hango GAYU BTC Na Masa Martani Cewa Yana Bukatar ILIMI Akasan Maganar AHMED XM Da Yake Cewa Masoyansa Su Saka UID Dinsu, Shi Kuma GAYU BTC Yace Ya Kamata XM Ya Sani WEB3 Wallet Babu UID.
Alamu Ya Nuna AHMED XM Baiji Dadin Ganin Yadda Mutane Suke Tunanin Karya Yake Musu, Yace yafi Karfin Yazo Media Yana Karyar Kananun Kudade ba, Cikin Takaici Ya Bayyana Cewa Basusan Kudin Agogon Hannunsa Bane.
Kwanakin Baya AHMED XM Ya fafata Da FOREX TRADERS, Yanzu Kuma fadan Cikin Gida ne Na Yan CRYPTO. Tuni Dai GAYU BTC Ya bayyana Cewa AHMAD XM Yayi BULOKIN Dinsa A X.
A Ganinku AHMAD XM Yayi Hakan Ne Don Jan Magana ko Kuma Kawai Mutane Ne Basu Fuskanceshi Ba ???