TAYAYA ZAKA INGANTA TSARON LAYIN DA KA BUDE BANK DASHI: A zamanin da ake amfani da wayoyin hannu wajen aiwatar da ayyukan banki da sauran mu’amaloli na sirri, tsaron layinka ya zama dole. Wannan cikakken jagora zai baka duk abin da kake bukata don inganta tsaron layinka da kuma kare bayananka masu muhimmanci.
Za mu tattauna yadda zaka samu PUK (Personal Unblocking Key), yadda zaka saita password don sim dinka, da kuma wasu dabarun tsaro da za ka iya amfani da su.
Mene ne PUK (Personal Unblocking Key)?
PUK shine lambar sirri wanda kamfanin wayarka ya baka don sake buɗe layinka idan ka kulle shi saboda yawan ƙoƙarin shigar da PIN da bai dace ba. Ba za ka iya shigar da PUK daga kanka ba; dole ne ka samu shi daga kamfanin wayarka.
Yaya Zaka Sami PUK Din Layinka?
Akwai hanyoyi da yawa da zaka iya samun PUK din layinka:
1. Duba Katin SIM (SIM Pack)
- Idan kana da ainihin katin SIM dinka, PUK yana rubutu a kansa.
- Yawanci yana cikin ɓangaren bayanan SIM, tare da lambar PIN da PUK.
*2. Amfani da 123# (Don Masu Amfani da MTN)
- Ka shigar da *123# a wayarka.
- Zaɓi Option 7 (Self Service).
- Daga nan, zaɓi Option 3 (Retrieve My PUK).
- Za a aika maka da PUK din ta hanyar SMS.
3. Kiran Customer Service
- Ka kira 180 (don MTN) ko lambar tallafin abokin ciniki na kamfanin wayarka.
- Ka ce kana buƙatar PUK din layinka.
- Za su yi maka wasu tambayoyi don tabbatar da cewa kai ne mai wayar.
- Idan ka amsa daidai, za su ba ka PUK din.
4. Amfani da Wani Layi
- Idan ba ka da wayar da za ka iya amfani da ita, ka ajiye lambar tallafin abokin ciniki a wurin da za ka iya kiransa.
- Ka kira su ta wani waya, ka ce kana buƙatar PUK din layinka.
- Za su yi maka tambayoyin tsaro, sannan su ba ka PUK din.
5. Ziyarar Ofishin Kamfanin Wayarka
- Ka je ofishin kamfanin wayarka (MTN, Airtel, Glo, ko 9mobile).
- Ka kawo wayarka da katin shaida (ID card) don tabbatar da cewa kai ne mai wayar.
- Za su baka PUK din a lokacin.
Lambobin USSD Da Zaka Danna Don Kulle Asusunka a Banki Idan An Sace Maka Waya
Yaya Zaka Saita Password Don Sim Dinka (SIM Security)?
Bayan ka sami PUK din, yana da muhimmanci ka saita password don sim dinka don hana wasu shiga layinka. Ga yadda zaka yi:
Don Masu Amfani da Android
- Shiga Setting na Wayarka
- Zaɓi “Connections” ko “Network & Internet”
- Shiga “SIM Manager”
- Danna “SIM Security”
- Saka Password da Kake So
Lura: Ba kowace waya ba tana da tsari ɗaya, don haka idan bakaga wannan hanyar, ka yi Google Search ko YouTube don neman yadda ake saita sim security a wayarka.
Don Masu Amfani da Keypad Phones (Wayoyin Tsoho)
- Shiga Setting na Wayarka
- Nemi “Security Settings”
- Zaɓi “SIM Security”
- Saka Password
Yadda Zaka Kare Bayanan SMS Da OTP Daga Masu Amfani da Wayarka
Wasu lokuta, OTP (One-Time Password) da ake aika wa wayarka na iya zama hanyar da masu amfani da wayarka za su iya amfani da su don shiga asusunka. Don haka, yana da muhimmanci ka kare su:
1. Boye Bayanan SMS a Lock Screen
- Shiga Setting na Wayarka
- Zaɓi “Apps” ko “Applications”
- Nemi “Messages” App
- Shiga “App Notifications”
- Zaɓi “Lock Screen Notifications”
- Danna “Hide Content”
2. Saita Password Don SMS App (Idan Wayarka Tana da Wannan Option)
- Shiga Setting
- Nemi “Privacy”
- Zaɓi “App Lock” ko “Message Security”
- Saita Password
Dalilin Da Yasa Tsaron Layinka Yake Da Muhimmanci
- Hana Wastar Layinka: Idan wani ya sami wayarka, zai iya amfani da layinka don yin kiran kuɗi ko samun bayanan sirri.
- Kare Bayanan Banki: Yawancin bankuna suna aika OTP ta SMS, don haka idan wayarka ba ta da tsaro, za a iya samun damar shiga asusunka.
- Hana Satar Bayanai: Masu satar bayanai na iya amfani da layinka don samun damar shiga wasu asusunka na sirri.
Ƙarin Shirye-shiryen Tsaro
- Kada Ka Ajiye PIN Ko PUK a Wayarka: A maimakon haka, rubuta su a wurin da ba za a iya samun su ba.
- Yi Amfani da Two-Factor Authentication (2FA): Wannan zai ƙara tsaro ga asusunka ta hanyar buƙatar lamba ta biyu kafin a shiga.
- Yi Amfani da App na Tsaro: Wasu apps kamar Google Authenticator suna ba da ƙarin tsaro ga OTP dinka.
Tsaron layinka yana da muhimmanci sosai, musamman idan kana amfani da shi don ayyukan banki. Ta hanyar bin waɗannan matakan, za ka iya tabbatar da cewa layinka yana da tsaro kuma ba za a iya amfani da shi ba tare da izininka ba. Idan kana da tambayoyi, faɗi mana a ƙasan comments!