Yadda Ake Ƙirƙirar NFTs Kyauta a 2025: Wannan Rubutu Zai Taimaka Maka Wajen Koyon Yadda Ake Kirkirar NFTs (Non-Fungible Tokens) Tareda Yadda Ake Amfani Dasu Da Yadda Ake Samun Kudi Dasu Cikin Sauki.
Note: This article is in Hausa. If you don’t understand Hausa, check the English version in the comments section. Thank you!
Yadda Ake Ƙirƙirar NFTs Kyauta ga Masu Son Farawa
Yadda Ake Ƙirƙirar NFTs Kyauta a 2025
Domin ƙirƙirar NFTs, ana buƙatar mutum mai basirar zane don ƙirƙirarsu.
Ƙirƙirar NFTs ba abu ne da kowa zai iya yi ba, gaskiya, sai dai idan kana da ƙwarewa a fannin zane-zane, wato graphic design. Masu ƙirƙira NFTs yawanci su ne graphic designers da ke da basira wajen ƙirƙirar hotuna mas ɗin kyau da iya amfani da kayan aikin zane kamar Photoshop, Illustrator, ko Procreate da sauransu.

Dalilin haka shi ne saboda NFTs suna buƙatar ingantaccen zane mai layers, tsari, da launuka masu kyau don su kasance masu jan hankali a kasuwa. Idan ba ka da ilimin zane, amfani da auto-generator tools kawai ba zai ba ka damar samar da zane na gaske masu ƙayatarwa da daraja ba.
Don haka, idan kana so ka shiga duniyar NFTs, yana da kyau ka fara koyon graphic design ko ka yi aiki tare da ƙwararrun masu zane. Wannan zai sa ka ƙirƙiri tarin NFTs masu inganci waɗanda za su ja hankalin masu saye da masu saka jari.
Mai Yasa Mutane Suke Siyan NFTs?
Mutane suna sayen NFTs saboda dalilai daban-daban, wanda suka haɗa da:
-
Ownership and Uniqueness
NFTs suna ba da tabbacin mallaka na kayan dijital wanda ba za a iya kwaikwayonsa ba. Kowane NFT yana da keɓantaccen hash a kan blockchain, wanda ke tabbatar da cewa ba zai yi kama da wani ba. -
Investment Opportunity
Wasu mutane suna sayen NFTs domin su sayar da su daga baya a mafi girman farashi. NFTs na iya haɓaka darajarsu idan sun shahara ko kuma an fi buƙatarsu a kasuwa. -
Utility and Access
Akwai NFTs da ake amfani da su don samun damar shiga wasu abubuwa na musamman kamar wasan kwaikwayo, events, ko ma wasu benefits na musamman a cikin wasu dApps. -
Collectibles and Art
Masu sha’awar fasaha da collectibles suna sayen NFTs domin su mallake su kamar yadda ake tara paintings, rare cards, da sauran abubuwan tarihi. -
Social Status and Flexing
Mutane da yawa suna sayen NFTs masu tsada don nuna matsayin su a duniya. Kamar yadda ake sayen motoci masu tsada ko kayan ado na alfarma, NFTs ma suna iya zama alamar alfarma. -
Gaming and Virtual Worlds
A duniyar GameFi, NFTs na iya wakiltar abubuwa kamar makamai, kayan sawa, ko fili a cikin metaverse. Wasu sukan saya domin su yi amfani da su a wasanni ko su sayar da su ga wasu players. -
Community Participation
Wasu NFTs suna da alaka da kungiyoyi ko DAOs, inda mallakar NFT ke ba mai shi damar kada kuri’a ko samun wasu fa fa’idodi a cikin community. -
Supporting Creators
NFTs suna ba da dama ga artists da content creators su sayar da ayyukansu ba tare da buƙatar kamfanoni masu sarrafa su ba. Wasu mutane suna sayen NFTs don tallafawa artists da masu ƙirƙira.
Tom, Bari Mu Dawo Cikin Topic Dinmu Kan Yadda Zaka Ƙirƙiri NFTs
Ga yadda za ka yi
Mataki Na Farko: Ƙirƙirar Zane a Cikin Layers
Don ƙirƙirar NFTs masu ban sha’awa, dole ne ka fara da ƙirƙirar zane a cikin layers.
Menene Layers?
Layers sune sassa daban-daban na hoto da za a iya haɗawa don samar da cikakken hoto. Kowanne layer yana wakiltar wani sashi ko fasali na NFT ɗinka.
Misali:
-
Layer 1: Zai iya zama background – wannan na iya zama launin bango ko zane.
Misali: Bango mai kalar yellow ko fari. -
Layer 2: Jiki – wannan na iya zama jikin halitta, kamar mutum, dabba, ko robot.
Misali: Jiki na mutum mai sanye da t-shirt, ko robot mai hannu na ƙarfe. -
Layer 3: Kai – kai na iya zama fuska, hula, ko wani sashi na fuska.
Misali: Kai mai hula, kai mara gashi, ko kai mai gilashi. -
Layer 4: Riga – riga na iya zama tufafi kamar t-shirt, jaket, ko hoodie.
Misali: T-shirt mai launin ja ko hoodie mai launin kore.
Yadda Ake Ƙirƙirar Layers
Za ka iya amfani da kowane app na graphic design (misali, Photoshop, Illustrator) don ƙirƙirar waɗannan layers daban-daban. Ajiye kowace sashi daban (bango, jiki, kai, riga) a matsayin file ɗin PNG ko JPG. Kowanne file zai wakilci wani layer na jikin hoton ne.
Mataki Na Biyu: Yin Amfani da StartNFT.app don Ƙirƙirar Tarin Avatar
Bayan ka ƙirƙiri layers ɗinka, lokaci ya yi da za ka haɗa su don samar da tarin NFT naka. Ga matakan a StartNFT.app:
-
Shiga site ɗin www.StartNFT.app
Bayan ka shiga, sai ka danna “Open Editor”: Wannan zai buɗe editor ƙirƙirar NFT. -
Danna “Create New Project”: Sai ka saka sunan aikin ka, misali “CoolAvatars”.
Sai ka zaɓi kalar aikin da kake son yi (misali, pixel art, illustration, da sauransu). Za mu zaɓi “Illustrations”. -
Uploading Layers ɗinka
A StartNFT.app, sai ka danna “Create Layer” don uploading sassan zanen ka.
Misali:-
Layer 1: Hoton background (misali, blue_background.png).
-
Layer 2: Hoton jikin NFT ka (misali, character_body_1.png).
-
Layer 3: Hoton kai (misali, head_1.png).
-
Layer 4: Hoton riga (misali, shirt_1.png).
Ka tabbatar da cewa ka saka hotunan da kuma sunan a cikin tsari (misali, bango a ƙasa, jiki a sama, da sauransu). Saboda idan ka saka layer 1 ɗinka suna body, sannan ka saka layer 2 head, to head ne zai fito a ƙasa, body kuma a sama.
-
-
Saita Rarities na Layers ɗinka
Menene Rarity a NFTs?Rarity na nufin matakin wuya ko na kankanta da wani abu ke da shi a cikin tarin NFTs. Wato, idan wani NFT yana da wasu siffofi ko abubuwa da ke da wahalar samu, to yana da rarity mai yawa. Idan kuma NFT ɗin yana da siffofi da ake samu da yawa, to rarity ɗinsa ƙanƙanta ne.Yadda Rarity ke Aiki a NFTs
A cikin NFT collection, kowane NFT yana da abubuwa daban-daban kamar:-
Launin background
-
Siffar jiki
-
Yanayin kai (hula, gashi, gilashi, da sauransu)
-
Tufafi
Idan wani abu yana da wahalar samu a cikin tarin NFTs, to yana da high rarity, kuma yana iya zama mai daraja sosai a kasuwa. Idan kuma yana da sauƙin samu, yana da low rarity, kuma darajarsa na iya zama ƙasa.Misali:
Idan aka ƙirƙiri NFTs guda 10,000, kuma daga cikinsu kawai 100 ne ke da golden hat, to waɗannan NFTs suna da high rarity, saboda kawai kashi 1% ne ke da wannan siffa. Wannan na iya sa su zama masu tsada a kasuwa.Muhimmancin Rarity a NFTs-
Yana ƙara daraja – NFTs masu high rarity suna iya samun ƙarin daraja da tsada.
-
Yana jawo masu saka jari – Mutane suna son NFTs da ke da wuya, saboda suna iya ƙara daraja a nan gaba.
-
Yana ƙara sha’awa – Idan wani NFT yana da siffofi na musamman, mutane za su fi sha’awarsa kuma za su fi son siyansa.
A editor, za ka saita yadda yawan kowace layer zai bayyana a tarin ka.
Misali: Idan kana da background guda 3, za ka iya so ɗaya ya zama mai wuya, don haka ka saita rarity zuwa 5% don wannan bango, kuma 95% don sauran biyu. Yi wannan ga kowace layer (bango, jiki, kai, riga) don saka yadda kowane layer daban-daban za su bayyana. -
-
Duba Collections ɗin NFTs ɗinka
Danna “Quick Preview” don ganin yadda NFTs ɗinka za su kasance lokacin da aka haɗa layers ɗin waje guda. -
Ƙirƙirar Collection na NFT ɗinka
Bayan ka gamsu da yadda komai yake, sai ka danna “Generate Collection”. StartNFT.app zai haɗa layers ɗin yadda ya kamata don ƙirƙirar NFTs masu ban sha’awa.
Kana da damar ƙirƙirar NFTs kyauta: StartNFT.app yana ba da damar ƙirƙirar har zuwa NFTs 100 kyauta. -
Fitar da Hotunan da Metadata
Menene Metadata?
Metadata na nufin bayanan wani abu. A cikin NFTs da blockchain, metadata na ƙunshe da duk bayanan da ke bayyane na NFT, kamar suna, siffa, launi, rarity, da sauran halayensa.Yadda Metadata ke Aiki a NFTs
A lokacin da aka ƙirƙiri NFT, ana haɗa metadata da shi don bayyana siffofinsa. Wannan bayanan yana iya haɗawa da:-
Sunan NFT (misali: Golden Warrior #0123)
-
Siffarsa (misali: robot, dragon, mutum)
-
Launi (misali: blue, red)
-
Rarity (misali: rare, legendary)
-
Kayan da aka yi amfani da shi (misali: gold, silver)
-
URI (Uniform Resource Identifier) – wuri inda hoton NFT ke ajiye akan IPFS ko wani wajen ajiya.
Wannan shine muƙoma kan topics ɗinmu.
Bayan an ƙirƙiri collection ɗin, za ka iya fitar da hotunan da metadata (bayanai game da kowace NFT kamar suna, bayani, halaye) don minting. -
Check: Yadda Content Creators Za Su Yi Social Media Monetization A Hausa: Sabbin Fasahohi Don Matasa
Mataki Na Uku: Minting da Sayar da NFTs a LaunchMyNFT.io
Yanzu da ka ƙirƙiri collections ɗinka, lokaci ya yi da za ka minting da lissafa NFTs ɗinka don sayarwa. Ga matakan a LaunchMyNFT.io:
-
Shiga site ɗin LaunchMyNFT.io
Sai ka yi Connect Wallet ɗinka, ka zaɓi blockchain da kake son amfani da shi (misali, SUI, Ethereum, Solana). -
Create New Collection
Danna “Create”: Wannan zai ba ka damar fara sabon tarin.
Shigar da bayanan collection ɗinka: bayanai kamar suna, bayani, da sauran bayanai masu mahimmanci. -
Upload your NFTs
Sai ka yi uploading hotunan NFTs ɗinka da metadata su waɗanda ka yi saving a file ɗinka daga StartNFT.app. -
Saita Whitelist da Farashi
Menene Whitelist?
A duniyar blockchain da NFTs, whitelist na nufin jerin sunayen mutane da aka ba dama ta musamman su yi wani abu kafin wasu. Wannan na iya zama damar siyan NFT kafin a buɗe wa kowa, ko kuma samun ragi, misali, idan 15 SUI ake ba da damar minting NFTs, to masu whitelist a 10 SUI za su yi minting.Tom, mu koma topic ɗinmu
Anan za ka iya saita whitelist don masu saye da farko da kuma iyakance yawan NFTs da za su iya minting. Hakanan, za ka saita farashin minting a nan ga public mints (misali, 0.1 ETH kowace NFT). -
Deploy Smart Contract
Minting NFTs ɗinka: Bayan ka saita komai, danna “Deploy” don minting NFTs ɗinka. Wannan zai ƙirƙiri smart contract da zai ba da damar sayarwa da mallakar NFTs a blockchain. -
Listing NFT ka a NFT Marketplace
Bayan ka gama, za ka zaɓi marketplace da za ka yi listing NFTs ɗinka depending on blockchain ɗin da ka yi deploying CA ɗinka. Idan ETH ne, za ka je OpenSea ko MagicEden. Idan Sol ne, za ka je MagicEden. Idan SUI ne, za ka je TradePort, da dai sauransu.
Note: Listing a marketplace yana buƙatar fees, amma ba yawa ba.
Duk da haka, ina so in yi video akan yadda za ku yi hakan idan na samu lokaci, saboda za a fi saurin fahimta a video akan rubutu. Amma shi ma wannan ɗin, idan kuka bi kuma kuka yi naku binciken tare da duba wasu videos ɗin a YouTube, na tabbata za ku fahimta.
To, wannan shine, Allah ya sa mu dace, Ameen summa Ameen.