Yadda Content Creators Za Su Yi Social Media Monetization A Hausa: Sabbin Fasahohi Don Matasa

Yadda Content Creators Za Su Yi Social Media Monetization A Hausa: Sabbin Fasahohi Don Matasa

Fasahar Social Media Monetization Ga Masu Shirya Bidiyo (Content Creators): Kun ga harkar Social Media Monetization din nan? Bari in ba da shata amsa ga duk content creators – maza da mata – waɗanda ke neman samun kuɗi ta hanyar sabbin fasahohin bidiyo.

6041635903379719540 6046277453061670035 6041635903379719539

Wannan shirin zai taimaka wa mutanen kauye da na birni su fahimci yadda za su yi bidiyo masu fa’ida waɗanda ke ba da:

  • Sabbin fasahohi
  • Ƙarfafawa (motivation)
  • Koyo daga gogewa
  • Kuɗi (Monetization)

Misalai Na Bidiyo Masu Kuɗi (Monetization Ideas) Social Media Monetization

1. Bidiyo Akan Noma Cikin Wayo

  • Ka ɗauki bidiyon manoma na ƙauye waɗanda suke noman masara, shinkafa, da sauran amfanin gona ba tare da kashe kuɗi da yawa ba.
  • Ka yi editing ka nuna fasaharsu ta musamman. Mutanen birni za su koya daga hakan, kuma ka sami Monetization.

2. Hira Da Masu Gyaran Motoci Da Injina

  • Ka yi hira da masu sana’ar gyaran mota, injina, ko waya – su ba da labarin yadda suka fara da kuma yadda suka ƙware.
  • Wannan zai ƙarfafa matasa waɗanda ke son irin wannan sana’a.

3. Bidiyo Akan Abincin Gargajiya

  • Yi bidiyo akan yadda ake yin Dambun Zogale, Rama, Tafasa, Daddawa (Traditional Maggi), da Yajin Kamshi (Traditional Royco).
  • Haɗa hira da likita don bayyana amfanin waɗannan abincin ga lafiya.
  • Mutane za su yi sha’awar, kuma Monetization din zai ci gaba.

4. Labarin Alarammomin Al-Qur’ani

  • Yi hira da Malaman Al-Qur’ani su ba da labarin tarihinsu da gwagwarmayar da suka yi.
  • Wannan zai ƙarfafa masu karatun Al-Qur’ani.

5. Binciko Alherin Manyan Mutane

  • Ka nemo mutanen da Sheikh Albani Zaria, Sheikh Dahiru Bauchi, Dr. Idris Abdul-Azeez, A.Y Shafa, da sauran masu kuɗi suka yi wa alheri.
  • Ka yi bidiyo da waɗanda aka yi musu alheri su faɗi abin da aka taimake su.
  • Wannan zai rage zargi cewa masu kuɗi ba sa taimakon jama’a.

6. Hira Da Daliban Jami’a Da Malamai

  • Yi hira da daliban MBBS, Law, Computer Science, da sauran fannoni su bayyana wahalarmu da sauƙin karatun su.
  • Ka nemi izinin shiga makarantu don ɗaukar hotuna ko bidiyo.

Kudi (Monetization) Da Fa’idodin Wannan Aikin

  • Za ka sami kuɗi daga tallace-tallace a kan bidiyonka.
  • Za ka taimaka wa mutane su fahimci alheri da fasaha.
  • Duniya za ta mori yawan mutane a matsayin alheri, ba sharri ba.

 

Duba: Yadda Za’a Dinga Samun Kudi Da Web3 Cikin Sauƙi


Abubuwan Da Ya Kamata Ka Yi Kafin Ka Fara

  1. Samun Kayan Aiki: Kamera, waya mai kyau, ko editing software.
  2. Nemi Izinin Mutum: Kafin ka yi hira da wani, nemi izininsa.
  3. Kashe Kuɗi Domin Bincike: Ka shirya tafiye-tafiye don ɗaukar bidiyo masu inganci.

Idan mutane ba su da yawa, ba za a sami alherin Social Media Monetization ba. Saboda haka, yawan mutane alheri ne – ka fara yin bidiyo yanzu!

 

CREDIT: Barrister Abdul-Hadee Isah

Scroll to Top